Labarai

NDLEA Ta Tarwatsa Wuraren Sayar da Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutane 56

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Kano, sun tarwatsa wurare da dama da ake sayar da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar, tare da kama mutane 56 a wani samame da aka gudanar tsakanin 6 zuwa 8 ga Fabrairu.

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar, ASN Sadiq Muhammad-Maigatari, ya bayyana cewa kwamandan NDLEA na jihar, Mista Dahiru Yahaya-Lawal, ya ce samamen wani ɓangare ne na “Operation Ramadan Mubarak”, wanda aka shirya domin rage yawaitar miyagun ƙwayoyi da tabbatar da zaman lafiya a lokacin Ramadan da ma bayan sa.

 

 

Samamen ya shafi yankuna da dama ciki har da Kofar Mata, Fagge, Kasuwar Rimi, Medile, Badawa da Sabon Gari, har ma da wasu wurare a wajen birnin Kano, domin rushe cibiyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba.

 

 

Jami’an sun kwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da wiwi (cannabis sativa), Exol-5, diazepam da pregabalin, yayin da aka miƙa ɗaya daga cikin wadanda aka kama, Yunusa Yasin mai shekaru 30, ga ‘yan sanda kan wani tsohon laifi da ya faru shekaru biyar da suka wuce.

 

 

Kwamandan NDLEA, Yahaya-Lawal, ya jaddada kudirin hukumar na ganin Kano ta zama jiha mara miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi domin kare al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button