Labarai

ICPC Ta Gano Wasu Kadarori a Masar da Ake Dangantawa da El-Rufai

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC sun gano wasu kadarori a ƙasar Masar da ake zargin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya mallaka.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an hukumar da suka nemi a sakaya sunayensu, saboda ba su da izinin yin magana a bainar jama’a, sun ce an gano kadarorin ne a wasu manyan unguwannin New Cairo.

Majiyoyin sun bayyana cewa yankin New Cairo na daga cikin wuraren da ke saurin bunƙasa a birnin Cairo, kuma an fi saninsa da gidaje masu tsada da kuma unguwannin da aka kulle domin tsaro da zaman lafiya.

 

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar ICPC ko daga bangaren tsohon gwamnan kan wannan zargi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button