Gwamnatin Jihar Kebbi ta mayar da martani mai zafi ga kalaman da fitaccen malami, Imam Bashiru Muhammad Jega, ya yi na sukar ayyukan gwamnatin jihar

A cikin bidiyon da ya ɗauki kusan mintuna bakwai, Imam Bashiru ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ba ta yi isassun ayyuka ba duk da kuɗaɗen da take samu.
Ya kuma ƙalubalanci ikirarin da Kabiru Haruna Gombe, sakataren ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (Izala) na ƙasa, ya yi cewa gwamnan Kebbi na kan gaba wajen tallafa wa addini.
Malamin ya tambayi adadin makarantun Islamiyya da gwamnatin jihar ta gina, tare da zargin cewa ana bai wa limamai ƙaramin alawus na kuɗi.
Haka kuma ya ce akwai bambanci tsakanin yadda ake biyan fansho ga tsoffin ma’aikata a Kebbi da wasu jihohi.
Sai dai kalaman nasa sun fusata gwamnatin jihar, inda mai bai wa gwamna shawara kan harkokin addinin Musulunci, Imrana Usman, ya ƙaryata zarge-zargen, yana mai cewa kalaman malamin cike suke da ƙarairayi.
Imrana Usman ya ce bai dace malami ya riƙa zuga jama’a ko haifar da ƙiyayya ba, yana mai jaddada cewa gwamnatin Kebbi ta gudanar da ayyuka da dama na tallafa wa addini da al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar ta gyara tare da gina masallatai sama da 150, baya ga tallafin da take bai wa masallatai a lokacin watan Ramadan.
Har ila yau, ya ce nasarar ceto ɗaliban Maga da aka sace ya samo asali ne daga haɗin gwiwar gwamnati da jami’an tsaro, yana mai cewa duk wanda ya san gaskiya ya kamata ya yaba wa ƙoƙarin da aka yi.
A ƙarshe, Imrana Usman ya shawarci Imam Bashiru da ya ji tsoron Allah tare da kauce wa kalaman da za su iya haddasa rikici a cikin al’umma.




