Labarai

DSP Mohammed Ladan Ya Tallafa wa Marayu 140 da Kayan Sallah a Yobe

Wani jami’in ɗan sanda, Mohammed Ladan, ya tallafa wa marayu 140 da kayan Sallah a Ƙaramar Hukumar Jakusko da ke Yobe

Da yake jawabi yayin rabon tallafin, DSP Mohammed Ladan ya bayyana cewa ya samu ƙwarin gwiwar gudanar da wannan aikin alheri ne da taimakon Allah tare da goyon bayan matarsa, Nadiya Mohammed Ladan.

 

Ya ce manufar tallafin ita ce tabbatar da cewa marayun sun yi bukukuwan Eid al-Fitr cikin farin ciki kamar yadda sauran yara masu iyaye ke yi.

 

DSP Ladan ya ƙara da cewa tallafa wa marayu da masu buƙata na daga cikin hanyoyin da za a inganta jin ƙai da taimakon juna a cikin al’umma, musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button