Jami’an KOSSAP Sun Kama Wani Matashi Da Ake Zargi Da Satar Wayoyi a Kano

Rundunar tsaro ta musamman dake yaƙi da ayyukan ɓatagari, fashi da makami, da satar wayoyi a jihar Kano, wacce aka fi sani da KOSSAP(Operation Zaman Lafiya Dole), ta samu nasarar damke wani matashi da ake zargi da ƙwarewa wajen sace wa mutane wayoyin hannu da kuma kayan sawa na mata.
Kwamandan rundunar, *Nura Salisu Sharaɗa* ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairu, 2026. Ya bayyana cewa jami’ansu sun yi nasarar cafke wanda ake zargin ne biyo bayan bincike da bin diddigin da suka gudanar.
A cewar Kwamanda Sharaɗa, binciken farko ya kai ga gano wani matashi daban a yankin *Sabuwar Mandawari* wanda shi ne ke sayen kayan satar, ciki har da wayoyin hannu, Atamfofi, da Leshi, daga hannun wanda ake zargin don amfanin kansa.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, matashin da ake zargi ya nuna matuƙar nadama game da ayyukansa.
Ya amsa cewa ya sayar wa abokin aikinsa aƙalla wayoyin hannu guda bakwai, baya ga kayan sawa daban-daban da ya sace.
Shi ma a nasa ɓangaren, matashin da ake zargi da sayen kayan satar ya bayyana cewa ya yi nadamar abin da ya aikata, inda ya sha alwashin cewa wannan shi ne karon farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kayan sata don kare mutuncinsa.
**Ahrasjo News © 2026**




