Labarai
Maharan Sun Kashe Mahaifin Tsohon Mataimakin Gwamnan Ebonyi

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa maharan da suka sace mahaifin tsohon Mataimakin Gwamnan Ebonyi Kelechi Igwe, sun kashe shi.
Mamacin, Francis Igwe, shi ne sarkin gargajiya na yankin Ndufu-Alike da ke ƙaramar hukumar Ikwo a jihar kafin rasuwarsa.
Rahotanni sun ce maharan sun sace sarkin ne a ranar Lahadi, 1 ga Maris, 2026, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci.
Jami’an tsaro sun ce suna ci gaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa da kuma tabbatar da an hukunta su.



