Labarai

Gwamnatin Kano ta kwace motocin Tsaffin kwamishinonin da suka bi tsarin Kwankwaso

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta fara aikin kwato motocin gwamnati da ke hannun wasu tsofaffin jami’an gwamnatin jihar, bayan zargin sun ƙi mayar da su duk da kammala wa’adin aikinsu.

Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ne ya jagoranci aikin a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026.

Ya bayyana cewa tun da fari Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya aika da wasiƙu ga tsofaffin jami’an da abin ya shafa, inda aka umarce su da su mayar da motocin gwamnati da ke hannunsu.

Sai dai, a cewarsa, wasu daga cikinsu ba su bi umarnin ba, lamarin da ya sa hukumar ta ɗauki matakin kwato motocin domin kare dukiyar al’umma da tabbatar da bin doka da oda.

Daga cikin tsofaffin kwamishinonin da aka kwato motocin a hannunsu akwai tsohon Kwamishinan Tsaro, Ibrahim Umar; tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabiu Kwankwaso; tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Yusuf Ibrahim Kofar Mata; tsohon Kwamishinan Jin Kai, Adamu Aliyu Kibiya; da kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo.

Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar dukkan matakan da doka ta tanada wajen kare kadarorin gwamnati, tare da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin tafiyar da mulki a Jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button