Labarai

Aƙalla mutum 25 aka kashe a hare-haren da ake zargin Boko Haram ta kai a Jihar Adamawa

Aƙalla mutum 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare guda biyu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a wasu sassan Jihar Adamawa

Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a garuruwan Madagali da Hong, waɗanda ke kusa da iyakar ƙasar Kamaru.

 

Yankunan dai na daga cikin wuraren da suka dade suna fuskantar hare-haren ƙungiyar Boko Haram tun bayan fara tashe-tashen hankulan da ta kaddamar a shekarar 2009.

Wani jami’in gwamnatin ƙaramar hukumar Madagali, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa wasu ‘yan bindiga a kan babura, da ake zaton mambobin Boko Haram ne, sun kai hari a wata kasuwa inda suka buɗe wuta kan jama’a, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 21 nan take.

Ya ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano yiwuwar samun wasu gawawwaki, kasancewar wasu daga cikin mutanen da suka jikkata sun tsere zuwa cikin daji, inda ake fargabar wasu na iya rasuwa sakamakon raunukan harbin bindiga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button