GCHRNN Ta Bai Wa Gwamnatin Kano Wa’adin Sa’o’i 24 Kan Zargin Cin Zarafin Dan Jarida

Kungiyar Global Community for Human Rights Network Nigeria (GCHRNN) ta yi kakkausar Allah-wadai kan zargin cin zarafin da aka yi wa dan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai, inda ta ce lamarin hari ne kai tsaye ga ’yancin aikin jarida da dimokuraɗiyya.
A cikin sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar, ta zargi wani jami’in gwamnatin Jihar Kano, Auwal Sani Rogo (SSR), da aikata cin zarafin a yayin wani taro da aka gudanar a gasar kamun kifi ta Argungu Fishing Festival.
Kungiyar ta bayyana cewa abin takaici ne yadda lamarin ya faru a gaban manyan jami’an gwamnati, amma har zuwa yanzu babu wani matakin ladabtarwa ko neman afuwa daga wanda ake zargi ko kuma daga gwamnatin Kano State.
GCHRNN ta ce wannan shiru da aka yi yana nuna rashin mutunta doka tare da yunkurin danne ’yan jarida a jihar.
Kungiyar ta bai wa gwamnatin Kano wa’adin sa’o’i 24 kacal da ta:
Dauki matakin ladabtarwa kan wanda ake zargi
Bayar da hakuri a hukumance ga dan jaridar
Tabbatar da kariya ga ’yan jarida a jihar
Ta kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, za ta garzaya kotu domin neman cikakken hakkinsa tare da daukar dukkan matakan doka da suka dace.
Haka zalika, kungiyar ta bukaci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano da ya gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.
Ta kara da cewa tana da majiya mai karfi da ke nuna cewa an shigar da korafi a gaban Kwamishinan ’Yan Sanda, amma wanda ake zargi bai amsa gayyatar da aka yi masa ba saboda dogaro da karfin mukami.
Kungiyar ta jaddada cewa wannan ba shi ne karo na farko ba, domin a kwanakin baya ma an samu cin zarafin dan jarida Aminu Halilu Tudunwada, lamarin da ta ce yana nuna yadda cin zarafin ’yan jarida ke kara kamari a jihar.




