Labarai

Rikicin Walida: Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Gargadi DSS Kan kin Bin umarnin Kotu

A sanarwar da Daraktan ƙasa na ƙungiyar, Abdullahi Bakoji Adamu, ya sanya wa hannu, an ce duk da bin hanyoyin doka da kuma umarnin kotu da aka bayar, har yanzu ba a maido da Walida ga iyayenta ba, lamarin da ƙungiyar ta ce ya saba wa dokokin kare haƙƙin bil’adama na ƙasa

Ƙungiyar ta yi nuni da tanade-tanaden United Nations cikin Universal Declaration of Human Rights (UDHR), musamman sashe na 3, 9 da 10, waɗanda suka tanadi haƙƙin rayuwa, ‘yanci da tsaro, da kuma samun shari’a ta gaskiya a gaban kotu .

Haka kuma ta ambaci tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 34(1), 35(1) da 36(1), da suka tabbatar da mutunci, ‘yanci da kuma haƙƙin samun shari’a ta gaskiya.

 

IHRC–RFT ta kuma jaddada muhimmancin adalci daga mahangar addini da tarbiyya, tana mai cewa tabbatar da adalci wajibi ne da ya rataya a wuyan shugabanni da hukumomi ba tare da nuna bambanci ba.

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnan Jihar Jigawa, sanatoci, ‘yan majalisun tarayya da na jiha, da kuma sarakuna da shugabannin addini da su shiga cikin lamarin cikin gaggawa domin tabbatar da bin doka da oda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button