Labarai

Farfesa Nazifi Abdullahi Darma Ya Dauki Nauyin Tallafin Magungunan Hawan Jini da Suga a Unguwar Darma

Al’ummar Unguwar Darma da kewayenta sun rabauta da tallafin magungunan hawan jini da ciwon suga kyauta, tare da samun damar gwajin lafiyarsu ba tare da biya ba a Asibitin Unguwar Darma.

Shirin duba marasa lafiya da bayar da magunguna kyauta ya samu tallafi ne daga Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, wanda ya dauki nauyin aikin gaba ɗaya domin tallafa wa al’umma, musamman a wannan wata na Azumi.

 

Da yake jawabi a madadinsa, Shafi’u Abdullahi Darma ya bayyana cewa halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da yawaitar cututtukan hawan jini da ciwon suga a tsakanin manya ne ya sa aka shirya wannan tallafi, domin rage radadin da al’umma ke ciki da kuma neman rahamar Allah a watan Azumi.

Ya ce sun ji daɗin addu’o’i da fatan alheri da al’ummar yankin ke yi wa Farfesa Nazifi, tare da gode musu bisa kauna da goyon baya.

A nasa jawabin, Mai Unguwar Darma, Mahmud Sani, wanda wakilinsa Ahmad Muhammad Sulaiman ya gabatar da sakonsa, ya yaba da wannan aiki na alheri, yana mai cewa babu abin da za su ce face godiya da fatan alheri ga Farfesa Nazifi bisa yadda yake tunawa da mahaifarsa ta hanyar ayyukan alheri.

Shi ma Bashir Mustapha Barwa, mataimaki na musamman ga Shugaban Majalisar Wakilai, ya yi kira ga ‘yan Unguwar Darma da su haɗa kai domin kawo ƙarin ayyukan cigaba a yankin, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kawo ayyukan alheri domin amfanin al’umma.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna farin cikinsu, suna masu yaba wa mai tallafin tare da yi masa addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.

Kimanin mutane sama da 200 daga Unguwar Darma da kewayenta ne suka amfana da tallafin magunguna da gwajin hawan jini da ciwon suga kyauta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button