Atiku Abubakar Ya Nuna Damuwar Karancin Fitowar Jama’a a Zaɓen Kananan Hukumomin Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwarsa kan ƙarancin fitowar jama’a a zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya, Abuja, da aka gudanar ranar Asabar, yana mai cewa hakan wata alama ce da ke nuna dimokuraɗiyya na fuskantar barazana a ƙasar.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Atiku wanda jigo ne a jam’iyyar ADC ya bayyana ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a matsayin hukunci mai tsauri kan yanayin dimokuraɗiyyar Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin da ke mulki.
Ya ce irin wannan ƙarancin halartar zaɓe a babban birnin ƙasa ba abu ne da ya faru haka kawai ba, sai dai sakamakon yanayin siyasa da ya gurbace ta hanyar rashin haƙuri, tsoratarwa da kuma raunana muradun ’yan adawa.
A cewarsa, gwamnatin mai ci ta rungumi manufofin da ke takaita sararin dimokuraɗiyya, da tsangwamar masu adawa, da matsa lamba ga masu sauya sheƙa, tare da haifar da yanayi inda ake kallon ra’ayoyin siyasa na daban a matsayin barazana maimakon gudummawa ga ci gaban ƙasa.
“Atiku ya ce, idan ’yan ƙasa suka rasa amincewa cewa ƙur’unsu na da tasiri, to dimokuraɗiyya na fara mutuwa.”
Ya ƙara da cewa abin da ake gani ba kawai sakacin masu zaɓe ba ne, illa sakamakon salon mulki da ke takura wa jam’iyyun adawa da ra’ayoyi mabambanta.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi gargaɗi cewa idan aka bar wannan yanayi ya ci gaba, zai iya janyo mummunar illa ga tsarin dimokuraɗiyya da aka shafe shekaru ana ginawa.
A ƙarshe, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da sauran masu kishin dimokuraɗiyya da su haɗa kai domin kare Jamhuriya da sake gina Najeriya.



