Labarai
Rabiu Musa Kwankwaso Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Ibrahim Shekarau

Tawagar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ta kai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ziyarar ta’aziyya sakamakon rasuwar ɗan uwansa.
A yayin ziyarar, Sanata Kwankwaso ya jajanta wa Sanata Shekarau da iyalansa bisa wannan babban rashi, tare da addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamacin, Ya kuma ba iyalai da ’yan uwa haƙurin jure rashin.
Kwankwaso ya bayyana cewa rashi mutuwa jarrabawa ce ga kowa, yana mai kira ga iyalai da su rungumi ƙaddara tare da ci gaba da yi wa mamacin addu’a.
Sanatan ya kai ziyarar ne tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, da sauran ’yan tawagarsa, inda suka nuna alhini da tausayi ga iyalan mamacin.



