Labarai

Zaɓukan Cike Gurbi a Kano: Jama’a Sun Nuna Halin Ko-In-Kula

Rahotanni na nuna nuna cewa an samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a zaɓukan cike gurbin ’yan majalisar dokokin jihar guda biyu da aka gudanar a ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal.

 

 

An gudanar da zaɓukan ne a rumfunan zaɓe 1,014 da ke faɗin ƙananan hukumomin biyu.

 

Duk da cewa jami’an zaɓe sun isa rumfunan kan lokaci domin fara aikin kada ƙuri’a, da dama daga cikin al’umma sun ƙi fitowa domin amfani da damar zaɓensu.

 

 

Bayanai sun kuma nuna cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (Independent National Electoral Commission) ba ta saka sunayen jam’iyyun NNPP, ADC da PDP a kan takardar kaɗa ƙuri’a ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button