Wata gobara da ta tashi da asubahin ranar Juma’a ta lalata akalla shaguna 50 a Kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose da ke unguwar Dakata a Jihar Kano

Shugaban kwamitin kashe gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe.
Ya bayyana cewa yawancin shagunan da abin ya shafa ƙananan sana’o’i ne, musamman masu harkar sarrafa mai da sake sarrafa robobi da nailan.
A cewarsa, har zuwa lokacin haɗa rahoton nan gobarar na ci gaba da tashi, yayin da ake jiran isowar jami’an Kano State Fire Service domin shawo kan lamarin.
“Daga binciken farko da muka yi, kimanin shaguna 50 sun riga sun lalace.
Mun sanar da hukumomin da abin ya shafa, kuma muna jin karar motar kashe gobara na tahowa,” in ji Chula.
Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a tantance adadin asarar da gobarar ta haifar ba, haka kuma ba a tabbatar da ko akwai waɗanda suka jikkata ba.
Lamarin ya sake tayar da hankalin ‘yan kasuwa a jihar, musamman ganin cewa bai wuce mako guda ba da wata babbar gobara ta shafi ‘yan kasuwa sama da 1,000 a Kasuwar Singer, ita ma a Kano.




