Bola Ahmed Tinubu Ya Nada Aminu Ado Bayero Shugaban Kwamitin Ciyarwar Ramadan na Ƙasa

An bayyana nadin ne lokacin da wata tawaga karkashin Babban Mai Tsare-Tsare na Ƙasa kuma Mataimakin Shugaban Kula da Fasaha a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta kai ziyara fadar Sarkin da ke Gidan Nassarawa a Kano.
Tawagar ta ce an zaɓi Sarkin ne bisa cancanta da dacewarsa da jagoranci.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya fitar, an bayyana cewa kwamitin bana ba na siyasa ba ne, illa tsari ne na Gwamnatin Tarayya domin hidimtawa al’umma a watan Ramadan.
Sanarwar ta ƙara da cewa aikin kwamitin zai haɗa da rabon kayan abinci kamar shinkafa, gero da man girki a faɗin ƙasar nan.
An kuma bayyana cewa a shekarun baya, aikin kwamitin ya fi taƙaita ne kan tara shugabanni domin yin buɗa-baki da shugaban ƙasa kawai, amma a wannan karo, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin faɗaɗa shirin zuwa rabon kayan abinci a dukkan shiyoyin Najeriya guda shida.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da manyan sakatarorin Gwamnatin Tarayya, daraktoci, sanatoci da ’yan majalisar tarayya, duk a ƙarƙashin kulawar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan wannan tsari, tare da fatan zai zama mai dorewa domin taimakawa al’umma.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa, tare da bada shawarwari da gudunmawa domin tabbatar da nasarar kwamitin.




