Labarai

Karamar Hukumar Kumbotso ta cimma yarjejeniya da rukunin kamfanin Mamuda Group of Companies domin gina sabon asibiti a unguwar Kureken Sani

Rahoton Arewa Updates ya bayyana cewa yarjejeniyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Karamar Hukumar, Abdullahi Ghali Basaf, ya fitar.

A cewarsa, yarjejeniyar ta tanadi bai wa kamfanin rangwamen wasu kudaden shiga na karamar hukuma, yayin da shi kuma zai gina asibitin a matsayin gudummawa ga al’umma a karkashin shirye-shiryen jin kai.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin dabarun haɗin gwiwa tsakanin ƙaramar hukuma da kamfanoni masu zaman kansu domin bunƙasa ayyukan jin ƙai da inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.

 

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa ziyarce-ziyarce da yake kai wa kamfanoni domin jawo zuba jari sun fara haifar da sakamako mai amfani, inda ya jaddada kudurin ci gaba da ƙarfafa irin wannan haɗin gwiwa domin amfanin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button