ICPC Ta Fara Bibiyar Ayyukan Mazabu a Kano da Jigawa

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa, Independent Corrupt Practices Commission (ICPC), reshen jihohin Kano da Jigawa, ta sanar da fara shirin bibiyar ayyukan mazabu da ‘yan majalisar tarayya ke sanyawa cikin kasafin kuɗin ƙasa a duk shekara.
Shugaban ICPC na Kano da Jigawa, Barista Ahmad Muhammad Wada, ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma hana karkatar da kuɗaɗen jama’a da aka ware domin ayyukan raya mazabu.
A cewarsa, hukumar za ta gudanar da ziyarce-ziyarce zuwa wuraren da aka ce an aiwatar da ayyukan domin tantance ko an yi su yadda ya kamata, bisa ka’ida da kuma abin da ke cikin kasafin kuɗi, tare da duba inganci da amfanin da al’umma ke samu daga cikinsu.
Barista Wada ya ce a Jihar Kano za su duba ayyuka 69, yayin da a Jihar Jigawa kuma za a tantance ayyuka 36 da ‘yan majalisar tarayya suka saka a kasafin kuɗi domin tabbatar da ko an aiwatar da su ko kuwa a’a.
Ya jaddada cewa ICPC ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na karkatar da kuɗaɗe ko aiwatar da ayyuka a takarda kawai ba tare da an yi su a zahiri ba.
Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su ba hukumar haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani zargi ko koke da ya shafi ayyukan mazabu a yankunansu.
Barista Wada ya ƙara da cewa jimillar kuɗaɗen da aka ware domin aiwatar da ayyukan raya ƙasa a jihohin biyu sun haura naira miliyan dubu 36.




