Barayin Shanu Sun Kashe Wani Magidanci a Rogo, Sun Bar Saƙon Barazana

Wasu da ake zargin barayin shanu ne sun hallaka wani magidanci, Malam Salisu Jibir Beli, yayin wani farmaki da suka kai gidansa a garin Beli, Ƙaramar Hukumar Rogo ta Jihar Kano.
Ɗan marigayin, Adamu Salisu Beli, ya shaida wa Arewa Updates cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare a makon da ya gabata, lokacin da ɓarayin suka kutsa cikin gidan dauke da makamai.
A cewarsa, maharan sun yi wa mahaifinsa duka har sai da ya fita a hayyacinsa, kafin daga bisani su kaɗa shanunsa su tafi da su.
Ya ce duk da an bi sahunsu, sun tsere, amma bayan kwana guda an gano wasu daga cikin shanun a yankin Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna.
Adamu ya bayyana cewa sun garzaya da mahaifinsu zuwa asibitin garin Rogo, inda daga nan aka tura su zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed Specialist Hospital da ke Kano
Washegari ne kuma suka samu gurbi a Aminu Kano Teaching Hospital, inda a nan ne Allah ya yi wa Malam Salisu rasuwa.
Ɗan mamacin ya roƙi hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin, musamman ma ganin cewa maharan sun bar saƙon barazana a gidan cewa “saura shi.”




