Labarai

DSS Takama matashin da ake zargi da Garkuwa da mutane ‘a Kano

Rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar ceto wani yaro mai shekaru biyar, Muhammad Haruna, daga hannun masu garkuwa da mutane a kauyen Danzaki da ke ƙaramar hukumar Minjibir.

An gudanar da aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:40 na yamma ranar Alhamis, bayan samun rahoton cewa an sace yaron tare da neman kuɗin fansa har naira miliyan goma sha biyar.

A yayin samamen, jami’an DSS sun cafke wani matashi mai suna Aminu Mukhtar, mai shekaru 20, wanda ake zargi da hannu a lamarin.

An kama shi ne yayin da yake tattaunawa da mahaifin yaron ta wayar salula kan batun biyan kuɗin fansa.

 

Wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya sace yaron domin neman kuɗin fansa.

Hukumar DSS ta jaddada aniyarta ta ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane, tare da kira ga al’umma da su rika bayar da rahoton duk wani abu da suka lura da shi domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button