Labarai

’Yan Bijilanti Sun Caka Wa Yaro Kusa a Zariya Kan Zargin Satar Kaza

Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a garin Zariya, inda wasu ’yan bijilanti suka caka wa wani yaro kusa mai tsawon inci biyar a kai bisa zargin satar kaza.

Lamarin ya shafi wani matashi mai suna Aliyu, wanda mahaifinsa Mallam Salisu Nuhu, da aka fi sani da Babande, mazaunin unguwar Limancin Kona, ya ce ya aike shi kasuwa domin sayar da kazar gidansu.

 

Sai dai a maimakon ya sayar da ita, wasu ’yan bijilanti suka kama shi tare da zarginsa da satar kazar, suka kai shi ofishinsu inda aka azabtar da shi.

 

Mahaifin yaron ya shaida wa Aminiya cewa bayan ya karɓo ɗansa daga hannun ’yan bijilantin, ya lura da wani mummunan rauni a kansa.

Aliyu ya bayyana masa cewa wani ɗan sa-kai mai suna Nuhu Dan Banga ne ya caka masa kusa a kai yayin da ake dukan sa, lamarin da ya sa ya suma a take.

An kuma kira mahaifin zuwa ofishin ’yan sa-kai na Unguwar Sirdi, inda aka buƙaci ya biya naira dubu biyar (₦5,000) a matsayin kuɗin beli.

Saboda rashin kuɗi, aka ba shi damar tafiya da ɗansa gida tare da umarnin dawo da kuɗin washegari.

A gida ne aka gano tsananin raunin da Aliyu ya samu, lamarin da ya sa aka kai shi wani asibiti mai zaman kansa, wanda daga bisani ya tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) Shika sakamakon tsanani da haɗarin raunin.

 

Babande ya ce sun kashe fiye da naira dubu dari takwas (₦800,000) wajen kula da lafiyar ɗansa, inda aka yi masa tiyata domin cire kusan da ta makale a kansa tsawon kwanaki 13.

 

Rundunar ’yan sandan Zariya ta tabbatar da kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, yayin da ɗayan kuma ya tsere.

’Yan sandan sun ce da zarar an kama wanda ya tsere, za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button