Labarai

An Gurfanar da Jami’an Civil Defence 3 a gaban kuliya Kan Zargin Kashe Abokin Aikinsu

Wata kotun majistare mai lamba 52 ta bayar da umarnin tsare wasu jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence su uku a gidan yari, kan zargin da ake musu na haddasa mutuwar wani abokin aikinsu.

Rundunar ‘yan sanda na tuhumar Zahraddin Muhd Abubakar Ya’u da Abbas Sagir, tare da wani mutum daya, da laifin da ya shafi mutuwar wani matashi a Unguwar Fagge kimanin watanni biyu da suka wuce.

‘Yan uwan mamacin sun zargi abokan aikin nasa da ke ofishin Civil Defence na Fagge da yi masa duka har lahira, bisa zargin sayar da kudi.

Hukumar ta Civil Defence ta sha musanta wannan zargi a baya.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga wata mai zuwa, inda za a ci gaba da shari’ar.

 

Muhasa Radio

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button