Labarai

Matsalar Tsaro Na Ci Gaba da Haddasa Mace-mace a Najeriya

Matsalar tsaro na ci gaba da kasancewa kan gaba cikin manyan abubuwan da ke janyo asarar rayuka a Najeriya, yayin da hare-hare da rikice-rikice ke ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Rikicin ƴanbindiga masu ɗauke da makamai, faɗace-faɗacen ƙabilanci da kuma hare-haren ta’addanci na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa mace-mace a ƙasar, wadda ake kira giwar Afirka saboda girma da tasirinta a nahiyar.

A watan Janairu na shekarar 2026, an kai wani mummunan hari a ƙauyen Kasuwan Daji da ke Jihar Neja, inda aka kashe aƙalla mutum 30, lamarin da ya sake nuna tsananin tabarbarewar tsaro a yankin.

Wani rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazarin harkokin tsaro a yankin Sahel, ya fitar ya nuna cewa kimanin mutum 661 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka sace mutum 475 a cikin watan farko na sabuwar shekarar 2026.

Masana na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button