Amasco FM Kano: Manyan ’Yan Jarida Mata Biyu Sun Ajiye Aiki

’Yan jaridar sun haɗa da Halima Abdullahi, wadda ke rike da mukamin Shugabar Sashen Labarai na gidan rediyon, da kuma Hidiya Salisu Ahmad, Mataimakiyar Shugabar Sashen Labarai.
Wata majiya daga cikin ma’aikatan Amasco FM, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa TST Hausa cewa ’yan jaridar sun ajiye aikinsu ne da son ransu, duk da cewa har zuwa yanzu ba su fito fili sun bayyana dalilansu ba.
Majiyar ta kara da cewa ana ta rade-radin cewa watakila sun dauki wannan mataki ne domin dogaro da kansu a harkar aikin jarida, sai dai har yanzu ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.
Wasu daga cikin ma’aikatan gidan rediyon sun bayyana cewa matakin ya jefa su cikin damuwa da alhini, musamman ganin yadda aka shafe lokaci mai tsawo ana aiki tare da su a matsayin abokan aiki.
Har zuwa hada wannan rahoto, hukumar gudanarwar Amasco FM ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da murabus din ’yan jaridar.




