’Yar Uwa Ga Gwamnan Kano Na Neman Taimakon Naira Miliyan 6 awajen jama’a Domin Ceto Rayuwarta

A yammacin ranar Asabar da ta gabata, kafar yaɗa labarai ta GTRHAUSA ta zanta da Hafsat Hashim Usman, wata mata da ke fama da mummunar lalurar ƙugu, wadda ke barazanar janyo mata rasa ƙafa matuƙa idan ba a samu taimako cikin gaggawa ba.
Hafsat ta shaida wa GTRHAUSA cewa ta shafe lokaci tana fama da ciwon ƙugu mai tsanani, wanda a halin yanzu ya kai matakin da ke hana ta samun isasshen bacci da walwala, inda ta ce “ciwon yau ba irin na gobe ba ne”, lamarin da ke ƙara tsananta mata rayuwa.
Ta bayyana cewa a matakin farko an yi mata tiyata a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, sai dai ba a samu nasarar da ake buƙata ba.
Daga nan ne likitoci suka tura ta zuwa Asibitin Ƙashi na Dala (Orthopedic Hospital), inda aka rubuta kudin aikin da za a yi mata, wanda ya kai Naira miliyan shida (₦6,000,000).
‘Yan uwa da makusantanta sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin neman taimako daga ’yan uwa na kusa da na nesa, amma hakan ya gagara.
Sun kuma ce duk da Hafsat tana da dangantakar jini da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, hakan bai kai ga samun wani gagarumin tallafi ba.
A cewarsu, an tura takardun neman taimako zuwa Gwamnatin Jihar Kano, tare da sanar da wasu jagororin zuriyar Gwani Mamman Zahraddin, sai dai har yanzu babu wani amsa ko ci gaba da aka samu, lamarin da suka bayyana a matsayin abin takaici.
Hafsat ta kammala da kira ga gwamnati, masu hannu da shuni, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma al’umma baki ɗaya da su taimaka mata domin samun damar yin aikin da zai ceci rayuwarta da makomarta.




