Magidanci Ya Hallaka Wani Mutum Bisa Zargin Soyayya da Matarsa a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta bayyana cewa abin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana, inda Alhaji Hassan Umaru, mai shekaru 50, ya kai wa Sukari Abdul, mai shekaru 45, hari da adda, wanda ya yi sanadiyyar mummunan rauni.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda sun garzaya wajen da abin ya faru tare da gaggauta kai wanda aka jikkata zuwa Asibitin Bularaba domin samun kulawar gaggawa.
Sai dai jami’an lafiya sun tabbatar da rasuwar Sukari Abdul nan take bayan isarsa asibitin.
Rundunar ta ce an cafka Alhaji Hassan Umaru a wurin da abin ya faru, tare da kwace addar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.
Haka kuma, an rufe kasuwar na ɗan lokaci domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da bincike na farko.
An mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin doka da ya dace bisa tanadin dokoki.
Rundunar ’yan sanda ta jaddada cewa za ta tabbatar da adalci ta hanyar bin doka da oda, tare da gargadin jama’a da su guji daukar doka a hannunsu komai irin halin da suke ciki.



