YARO ƊAN SHEKARA UKU YA RASA RANSA BAYAN FAƊUWA CIKIN RIJIYA A KANO

Wani yaro ɗan shekaru uku, mai suna Abdura’uf Badamasi, ya rasu bayan da ya faɗa cikin wata rijiya a ƙauyen Wangara, da ke ƙaramar hukumar Tofa a Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7:50 na safiyar Juma’a, 30 ga watan Janairu, wanda ya sanar da faruwar lamarin.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, wani mutum mai suna Ɗan Asabe Rabiu ne ya kira domin sanar da aukuwar hatsarin.
Bayan karɓar kiran, hukumar ta tura tawagar ceto daga hedikwatarta zuwa wurin da abin ya faru.
Da isarsu, jami’an sun samu bayanai cewa tun daga yammacin ranar Alhamis aka rasa yaron, inda iyayensa ke zargin cewa ya faɗa cikin rijiyar.
Jami’an kashe gobara sun shiga cikin rijiyar tare da fitar da yaron, amma an same shi baya cikin hayyacinsa kuma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.




