Najeriya Ta Fuskanci Sake Katsewar Wutar Lantarki Sakamakon Lalacewar Babban Layi

Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin wutar lantarki na ƙasar, a ranar Talata.
Wannan shi ne karo na biyu a shekarar 2026 da babban layin ke fuskantar irin wannan matsala, wadda ta haifar da katsewar wuta a sassa da dama na ƙasar.
Lalacewar layin ta fara ne tun a ranar Juma’a da ta gabata.
Masana da hukumomi sun danganta matsalar ne da tangarɗar na’urori da rashin cikakken gyare-gyare da kulawa ga manyan layukan wuta.
Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya.
A halin yanzu, babu cikakken bayani kan abin da ya janyo wannan lalacewa, sai dai hukumomi sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin matsalar da kuma daukar matakan gyara.




