Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Zai Koma Jam’iyyar APC a Ranar Litinin

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na shirin komawa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a makon da ya gabata.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya futar
Sanarwar ta tunatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi niyyar shiga jam’iyyar APC tun a shekarar 2014, lokacin da ya lashe zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, kafin daga bisani ya janye wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An rawaito Gwamna Abba Kabir Yusuf yana cewa komawarsa APC za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da ta tarayya, da hanzarta ayyukan raya ƙasa, da inganta haɗin kai a fannin tsaro, tare da ƙara kyautata ayyukan jin daɗin al’umma a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya, kwanciyar hankali da haɗin kan siyasa a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan zai yi rajista a hukumance a jam’iyyar APC a Kano a ranar Litinin, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar 22, ‘yan Majalisar Wakilai takwas, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Haka kuma ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai ƙaddamar da aikin rajistar APC ta hanyar lantarki (e-registration) a jihar Kano a wannan rana.




