Labarai

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ya Ziyarci Sansanonin Sojoji a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau I. Jibrin, ya ziyarci sansanonin jami’an tsaro a wasu sassan ƙananan hukumomin Gwarzo, Shanono da Tsanyawa da ke yankin Kano ta Arewa, domin ƙarfafa gwiwar dakarun da aka tura yankin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga daga jihohin makwabta.

 

Ziyarar ta gudana ne a ranar Lahadi, bayan da ‘yan bindiga suka kai hare-hare a wasu yankuna na ƙananan hukumomin guda uku, lamarin da ya sa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron farar hula domin dakile ayyukan ‘yan bindigar.

 

A wata sanarwa da mai ba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, ya ce Sanata Barau ya isa Kano da misalin ƙarfe 7 na safe, inda kai tsaye ya nufi sansanin jami’an tsaro da ke Lakwaya Ward a ƙaramar hukumar Gwarzo.

 

A yayin ziyarar, Sanata Barau, tare da Kwamandan Garrison na Brigade ta Uku ta Rundunar Sojin Ƙasa da ke Kano, Laftanar Kanar I. Ekoh, da sauran manyan jami’an tsaro, sun duba faretin dakarun da Kwamandan rundunar haɗin gwiwa (JTF) na Gwarzo, Laftanar Abdullahi Sadiq, ya jagoranta.

 

Bayan kammala faretin, Sanata Barau ya yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewa da sadaukarwa da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa saurin amsa kiran da aka yi masa na tura jami’an tsaro yankin.

 

Ya ƙarfafa gwiwar dakarun da su ci gaba da matsa lamba kan ‘yan bindigar da ke tayar da hankalin al’umma, yana mai kira da a bi su ko’ina suke domin murƙushe su da kawar da su daga yankin.

 

Sanata Barau ya kuma yi kira ga al’ummomin yankin da su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya, yana mai jaddada cewa nasarar yaƙi da ‘yan bindiga na buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa.

Daga sansanin Lakwaya, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ya ziyarci wasu sansanonin jami’an tsaro a mazabu daban-daban na ƙaramar hukumar Shanono da kuma Tsanyawa, inda ya yi wa jami’an jawabi tare da ƙarfafa musu guiwa.

Haka kuma, ya gana da shugabannin al’umma a yankin Faruruwa da ke Shanono, inda suka nuna godiyarsu bisa tura jami’an tsaro yankin da kuma sauran ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button