NNPP Tayi kakkausar suka dan gane da Ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf Daga Jam’iyya

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta al’ummar jihar Kano da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, inda ta ce a ra’ayinta, ficewar gwamnan daga NNPP na nuni da cin amanar masu kaɗa ƙuri’a, waɗanda suka mara masa baya bisa tafiyar siyasar Kwankwasiyya da ya daɗe yana ciki.
A cewar jam’iyyar, al’ummar Kano sun zaɓi Abba Kabir Yusuf ne saboda biyayya da jajircewarsa ga tafiyar Kwankwasiyya tsawon shekaru, amma a yanzu ya juya wa wannan amana baya.
“Mun shiga matuƙar takaici ganin yadda Gwamna Abba, wanda aka damƙa masa jagorancin al’ummar Kano bisa sadaukarwa da biyayya da ya nuna wa tafiyar Kwankwasiyya tsawon lokaci, yanzu ya zaɓi ya ci amanar wannan amana,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar NNPP ta kuma yi gargaɗin cewa matakin na gwamnan na iya jefa jihar Kano cikin hannun wasu da ta bayyana a matsayin waɗanda suka daɗe suna adawa da ci gaba da muradun al’ummar jihar.
Sai dai jam’iyyar ta yi kira ga magoya bayanta a faɗin jihar Kano da su kwantar da hankalinsu, su bi doka da oda, tare da guje wa duk wani abu da zai iya haifar da rikici ko tashin hankali na siyasa ko na zaman rayuwa.




