Siyasa

Gabanin 2027: Makinde Ya Warware Jita-jitar Komawa APC

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa ziyarar ta kasance domin tattauna batutuwan da suka shafi mulki da ci gaban ƙasa, ba batun siyasa ba.

 

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

 

Duk da ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP zuwa APC a baya-bayan nan, Makinde ya jaddada cewa har yanzu yana nan daram a PDP.

 

Ya ce ci gaban Najeriya ya fi batun bambancin jam’iyya muhimmanci, inda ya yi kira ga haɗin kai tsakanin shugabanni domin amfanin ƙasa gaba ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button