Sojojin sun ceto fasinjoji 18 daga hannun ‘yan fashin ruwa

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na 13 Brigade sun ceto fasinjoji 18, ciki har da jarirai biyu, daga wani jirgin ruwa da ‘yan fashin ruwa suka kama a ranar 11 ga Janairu, 2026, a yankin kogunan Kamaru.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X.
Sanarwar ta bayyana cewa ‘yan fashin ruwa sun kai wa jirgin da ke tafe daga Najeriya zuwa Kamaru hari a gaɓar tashar kamun kifi ta Kombo, lamarin da ya haifar da musayar wuta bayan sojoji sun bi su.
Daga bisani, ɗaya daga cikin jiragen ‘yan fashin ya kife, lamarin da ya sa suka tsere suka bar fasinjojin, inda sojoji suka ceto su lafiya.
Kwamandan 13 Brigade, Brigadiya Janar PO Alimikhena, ya yaba da jajircewar sojojin tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.




