Gwamnan Sokoto Ya Nemi Goyon Bayan Jama’a Domin Yaki da ‘Yan Bindiga

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya buƙaci al’ummar jihar da su ƙara bai wa jami’an tsaro goyon baya ta hanyar samar da bayanan sirri domin magance matsalar hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a saƙonsa na sabuwar shekara, inda ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen ganin shekarar 2026 ta fi 2025 ta fuskar tsaro da ci gaba. Ya ƙara da cewa an samar da tsare-tsare na musamman domin tattara bayanan sirri da daƙile hanyoyin da maharan ke bi, musamman a ƙananan hukumomi 13 da ke fama da matsalar tsaro.
Har ila yau, Aliyu ya ce gwamnatinsa za ta ba da muhimmanci ga inganta ababen more rayuwa, lafiya, jin ƙai da ilimi, ciki har da gina da gyaran makarantun Islamiyya, tare da kammala manyan tituna kafin ƙarshen zangon farko na shekarar 2026.




