Labarai

”Duk wanda bai zabi Tinubu a zabe mai zuwa ba, ba cikakken musulmi  bane

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sani Yahya Jingir, ya jawo muhawara a tsakanin al’umma bayan furucin da ake danganta masa na cewa duk wanda bai zabi Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa ba, ba cikakken Musulmi ba ne.

Rahotanni sun nuna cewa kalaman sun bazu sosai a kafafen sada zumunta,  kamar yadda jaridar APN  ta rawaito inda suka haifar da muhawara mai zafi tsakanin mabiyansa da kuma masu sukar wannan matsayi.

 

Wasu na ganin furucin ya hada siyasa da addini ta hanyar da ka iya haddasa rikici, yayin da wasu ke kare shi da cewa ra’ayin sa ne kawai a matsayin jagora na addini.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button