Siyasa

APC Ta Karyata Rahoton Fitar da Farashin Fom ɗin Zaɓen 2027

Jam’iyyar APC ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke cewa an fitar da farashin fom ɗin takarar zaɓen shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar a Abuja, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, tare da zargin cewa an ƙirƙire shi ne domin yaudarar jama’a.

Sanarwar ta jaddada cewa babu wani mataki ko hukunci da jam’iyyar ta ɗauka dangane da sayar da fom ko bayyana farashinsa domin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci mambobinta, kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma da su yi watsi da rahoton baki ɗaya, tare da dogaro da sahihan bayanai daga jam’iyyar.

 

APC ta ƙara da cewa duk wata sanarwa a hukumance za ta fito ne ta hanyoyin sadarwa da aka amince da su kawai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button