Labarai
‘Yan Sanda Sun Ƙuduri Aniyar Ƙarfafa Tsaro a Abuja

Sabon Kwamishinan ‘yan sanda na FCT, Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin da ya kama aiki a matsayin kwamishina na 35 a yankin.
Ya jaddada cewa rundunar za ta bullo da sabbin dabarun tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin birnin.
Sanusi ya karɓi ragamar aiki ne daga hannun Miller Dantawaye, wanda aka ɗaga darajarsa zuwa Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG), tare da tura shi hedikwatar rundunar
Sabon kwamishinan na FCT ana sa ran zai ƙarfafa tsarin tsaro tare da inganta ayyukan sintiri da sauran matakan tsaro a faɗin Abuja, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mazauna yankin.



