Ketare

Iran ta gargadi Birtaniya kan bai wa Amurka sansanoninta

Iran ta shaida wa Birtaniya cewa bai wa Amurka damar yin amfani da sansanoninta tamkar “shiga cikin yaki” ne, kamar yadda ministan harkokin wajen Iran din ya shaida.

 

Abbas Araghchi ya yi waya da takwaransa na Birtaniya, Yvette Cooper inda ya shaida musu cewa duk wani taimako da Birtaniyar ta bai wa Amurka to zai iya “kara ta’azzara2 yanayin ne.

 

Araghchi ya kuma zargi Birtaniya da sauran kasashen Turai da “nuna son kai” kan abin da ya kira “tsokana ta kurukuru” da Amurka da Isra’ila ke yi.

 

Rahotanni na cewa Araghchi ya kuma yi kakkausan suka ga Birtaniya bisa kin sukar hare-haren Isra’ila a ma’adanar iskar gas ta South Pars na Iran.

 

BBC

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button