Labarai

Sarkin Musulmi Ya Umarci Al’umma Su Fara Duba Jinjirin Watan Shawwal

Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi, ya umarci al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara duban jinjirin watan Shawwal daga yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan na shekarar 1447 Hijira.

Ranar dai ta yi daidai da 18 ga Maris, 2026, kuma ganin jinjirin watan ne zai tabbatar da ranar gudanar da bukin Eid al-Fitr na bana.

 

Shugaban kwamitin harkokin addini na Sokoto Sultanate Council, kuma Wazirin Sokoto, Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

A cewarsa, duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal da idonsa ana bukatar ya sanar da Hakimi ko Uban ƙasa mafi kusa da shi domin a tattara bayanan shaidar ganin watan, sannan a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.

 

Ya kara da cewa idan aka ga jinjirin watan a ranar Laraba, to za a gudanar da Sallar Idi a ranar Alhamis.

 

Amma idan ba a ga watan ba, za a cika kwanaki 30 na Ramadan, wanda hakan ke nufin za a yi Sallar Idi a ranar Juma’a.

 

Farfesa Sambo Wali Junaidu ya kuma yi addu’ar Allah Ya taimaka wa al’umma wajen gudanar da wannan muhimmin aiki na addini cikin nasara.

 

A halin yanzu dai al’ummar Musulmi a sassa daban-daban na ƙasar na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama ta bana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button