United States da Israel Sun Kai Hare-hare kan Iran

Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai sun nuna cewa Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran, lamarin da ya haddasa tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa an ji ƙarar manyan fashewa har uku a birnin Tehran, babban birnin ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ce ya samu rahotannin faɗuwar makamai masu linzami a wasu sassan birnin.
A gefe guda, kafofin yaɗa labaran Amurka da na Isra’ila sun ce ƙasashen biyu ne suka haɗa gwiwa wajen aiwatar da harin.
Tun da daɗewa Amurka ke barazanar ɗaukar matakin soja kan Iran dangane da shirinta na nukiliya.
A makon da ya gabata ma, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Iran wa’adin kwanaki 10 da ta cimma yarjejeniya kan shirin nata, ko kuma ta fuskanci matakin soja.




