Siyasa

Gwamnan Nasarawa ya ayyana wanda yake so ya gaje shi

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda yake so ya gaje shi a zaben gwamna mai zuwa.

 

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ali Abare, ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da mukarrabansa da shugabannin hukumomin gwamnati a Lafia.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sule ya ce an dauki sama da shekara guda ana tuntuba da bangarori daban-daban ciki har da matasa, mata, sarakunan gargajiya da ‘yan jam’iyya kafin zabar Wadada a matsayin mafi dacewa.

 

Ya kara da cewa an takaita zabin zuwa ‘yan takara uku masu karfi kafin daga bisani a zabi Wadada, tare da jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyyar APC.

 

Gwamnan ya bukaci duk masu ruwa da tsaki su marawa zabin baya ba tare da nuna bambanci ba, yana mai gargadin kada a raina sauran ‘yan takarar da ba a zaba ba.

 

Haka kuma, ya nuna kwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasara a jihar a zaben 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button