Labarai

INEC Ta Sanya 20 Ga Fabrairu, 2027 A Matsayin Ranar Zaɓen Shugaban Ƙasa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027 a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gaba a Najeriya.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja.

Ya ƙara da cewa za a gudanar da zaɓukan ‘yan majalisun tarayya a ranar guda da zaɓen shugaban ƙasar.

Haka kuma, ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 6 ga watan Maris, 2027.

 

Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 sun kammala, tare da jaddada aniyar INEC na gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button