Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 ga watan Maris a Matsayin Ranar Fara Hutun Sallah Ga Dalibai

Gwamnatin Kano ta ayyana ranar Lahadi 1 ga Maris, 2026 a matsayin ranar fara hutun Sallah ga daliban firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.
Rahoton Arewa Updates ya nuna cewa sanarwar na kunshe ne a cikin takardar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Musbahu Aminu Yakasai, ya fitar a ranar Laraba 25 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa zangon karatu na biyu zai kare a ranar Asabar 28 ga Fabrairu, 2026. Haka kuma, an bukaci iyaye da masu kula da daliban makarantun kwana da su dauke su zuwa gida tun daga safiyar Juma’a 27 ga Fabrairu, 2026.
A cewar gwamnatin, daliban makarantun kwana za su koma makaranta a ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, yayin da daliban jeka-ka-dawo za su koma a ranar Litinin 23 ga Maris, 2026.
Gwamnatin ta umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su bi wannan jadawali, tare da gargadin cewa za a dauki mataki kan duk wata makaranta da ta saba wa umarnin.


