Rikici Ya Fara Tunkaro Jam’iyyar APC a Kano Bayan Sauyin Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Alamun rikicin sun fara bayyana ne a yayin tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi da aka fara gudanarwa a wasu ƙananan hukumomin jihar, inda rahotanni ke nuna samun saɓanin ra’ayi da rarrabuwar kai a tsakanin mambobin jam’iyyar.
Shugabancin jam’iyyar APC a matakin jiha ne ya bayar da umarnin gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki, a wani yunƙuri na ɗinke barakar da ke ƙoƙarin ɓullowa, gabanin babban zaɓen cikin gida na jam’iyyar da ke tafe.
Sai dai duk da wannan mataki, masana siyasa sun bayyana cewa tuni aka fara ganin alamun rikici, musamman duba da yadda ake samun sabon sauyin siyasa a jihar Kano bayan shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa, idan har shugabancin jam’iyyar bai ɗauki matakai masu zurfi na sasanci da haɗa kai ba, to rikicin na iya ƙara tsananta, lamarin da zai iya shafar haɗin kan APC a Kano nan gaba.
Rahotanni dai na nuni da cewa, wasu daga cikin tarukan masu ruwa da tsaki an gudanar da su ne a rarrabe, abin da ke ƙara nuna irin ƙalubalen da jam’iyyar ke fuskanta wajen cimma cikakken daidaito a tsakanin ‘ya’yanta.
B B C HAUSA




