Siyasa

Na hannun daman Ganduje ya fice daga APC zuwa ADC

Salihu Tanko Yakasai, daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ADC.

 

Yakasai ya sanar da ficewar ta sa ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook a safiyar yau Litinin.

 

Ya kuma wallafa hoton katin jam’iyyar ADC da ya yi rijista a mazaɓarsa.

 

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Salihu Tanko Yakasai ya taba ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PRP a Shekarar 2022, bayan zaben 2023 kuma ya koma APC yanzu kuma ya sake ficewa daga jam’iyyar zuwa ADC.

 

Ga sakon da ya walllafa

 

Bayan shawarwari da tuntubar yan’uwa da abokan arziki da sauran yan gwagwarmayar siyasa abokan tafiya, mun yanke shawarar shiga Jam’iyar ADC Sabuwar Tafiya! Tuni, na mika takardar fita daga jam’iyar APC tare da yin rijista a sabuwar jam’iyar mu ta ADC.

 

Wanda suke da sha’awar shiga jam’iyar ADC zasu iya yin rijista ta wayar su a wannan link din www.adcregistration.ng cikin kankanin lokaci zaka samu katin ka na dan jam’iya!

 

Muna rokon Allah Ubangiji Ya sa hakan ne mafi alheri, Ya kuma sa jam’iyar ADC ta kafa gwamnati sama da kasa, Ya kuma sa hakan ya zama alheri ga yan Najeriya baki daya amin!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button