Gwamnatin Tarayya Za Ta Hada Kai da makarantar koyar da aikin Hajji ta Talbiya don Wayar da Kan Maniyyata Hajjin Bana

Darakta Janar na Makarantar Nazarin Hajji da Umrah ta Talbiya, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf, a ofishinsa da ke Abuja.
A yayin ziyarar, Dr. Harun Ibn Sina ya taya sabon shugaban NAHCON murna bisa nada shi da aka yi, inda ya bayyana cewa nadin ya zo ne bisa cancanta da kwarewa.
Ya kuma yi bayani kan muhimman ayyukan Talbiya, musamman a bangaren ilimantarwa da wayar da kan maniyyata domin samun ingantacciyar Hajji (Hajj Mabrur).
Shi ma a nasa bangaren, Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya nuna jin dadinsa da wannan ziyara, tare da yabawa manufofi da ayyukan makarantar Talbiya.
Ya kuma jaddada aniyar hukumar wajen hada kai da Talbiya a fannoni daban-daban, domin inganta ayyukan Hajji ta fuskar addini, zamantakewa da gudanarwa.
Hakazalika, ya bayyana cewa hadin gwiwar da za a kulla tsakanin bangarorin biyu zai taimaka wajen kara kyautata ayyukan Hajji a Najeriya baki daya.
Ziyarar ta samu halartar wasu jami’an Talbiya da suka hada da Mataimakin Darakta Janar, Dr. Aliyu Musa Kibiya, da kuma wasu mambobin NAHCON.



