Labarai
Majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2026 a wasu sassan ƙasar

A wata sanarwa da Sakataren Kwamitin Ganin watan Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar, ya bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ne ya sanar da ganin watan a madadin Muhammad Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi, wanda ke balaguro a ƙasashen waje.
Sanarwar, wadda aka wallafa a shafin Tuwita na kwamitin ganin wata, ta ce an tabbatar da ganin watan ne bayan samun sahihan rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci a wasu jihohin Najeriya.
Dangane da hakan, an bayyana cewa gobe Laraba 18 ga Fabrairu, 2026, za ta kasance ranar 1 ga watan Ramadan, inda al’ummar Musulmi za su fara azumin watan mai alfarma.




