Gwamna Uba Sani Ya Sha Alwashin Ceto Mutanen da Aka Sace a Kajuru

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin ganin an ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali, da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za mu huta ba har sai mun tabbatar da cewa an ceto kowane mutum da wannan mummunan aiki ya shafa kuma an dawo da su cikin koshin lafiya zuwa ga iyalansu.”
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Lahadi da ta gabata, inda wasu ‘yan bindiga suka kai samame a ƙauyen na Kurmin Wali da sanyin safiya, suka yi awon gaba da mutane da dama.
Harin ya haifar da firgici da tashin hankali a tsakanin al’ummar yankin.
Kodayake rahotanni marasa tushe na nuni da cewa adadin mutanen da aka sace na iya kaiwa sama da 170, har yanzu hukumomin tsaro da gwamnatin jihar ba su fitar da ainihin adadin mutanen da abin ya shafa ba a hukumance.
Da farko an samu tsaiko wajen tabbatar da faruwar lamarin daga hukumomi, amma daga bisani sun amince da aukuwar sa, kuma yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike da ayyukan ceto.
Al’ummar jihar Kaduna na ci gaba da addu’o’in fatan ganin an ceto wadannan bayin Allah cikin gaggawa kuma a dawo da zaman lafiya a yankin.



