Mustapha Rabiu Kwankwaso da wasu karin tsofaffin Kwamishinoni sun maka gwamnatin Kano a kotu

Wasu tsofaffin kwamishinonin Gwamnatin Jihar Kano da suka yi murabus tare da bin jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, sun kai ƙarar gwamnatin jihar kotu domin neman a biya su haƙƙoƙinsu.
Rahoton da Arewa Updates ta rawaito ya nuna cewa matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da tsofaffin kwamishinonin suka fitar, inda suka bayyana cewa sun fara neman a biya su haƙƙoƙinsu ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, amma ba su samu wata amsa ba.
A cewar sanarwar, suna neman a biya su haƙƙoƙin da suka shafi aikin da suka gudanar a matsayin kwamishinoni, da kuma kuɗaɗen da suka kashe tare da amfani da motocinsu na tsawon sama da shekaru biyu yayin da suke kan muƙami.
Sun ƙara da cewa sun yanke shawarar kai ƙarar kotu ne domin a tilasta wa gwamnatin jihar ta biya su dukkan haƙƙoƙinsu na motoci da kuɗaɗe, kamar yadda dokar Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission Act 2023 (RMAFC Act 2023) ta tanada.
Tsofaffin kwamishinonin sun jaddada cewa matakin shari’ar da suka ɗauka ba wai don tayar da hankali ba ne, sai don neman adalci da bin doka wajen tabbatar da an biya su abin da ya dace da su.



