’Yan Fansho a Jihar Jigawa Sun Karɓi Kashi na Biyu na Kuɗaɗen Giratuti Sama da Naira Biliyan 1.4

Hukumar Kula da Fansho ta Jihar Jigawa ta raba sama da Naira biliyan 1.4 a matsayin kashi na biyu na kuɗaɗen giratuti ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati 564 da suka yi ritaya daga aiki a jihar.
An gudanar da rabon kuɗaɗen ne a ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026, a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
Da yake jawabi ga waɗanda suka amfana, Babban Akanta na Jihar Jigawa, Alhaji Abdullahi A.G. Shehu, ya bayyana cewa tun daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu, Gwamna Malam Umar Namadi ya zuba sama da Naira biliyan 11 domin ƙarfafa tsarin fansho na gudunmawar haɗin gwiwa, lamarin da ya sanya Jigawa ta zama abin koyi a fannin tafiyar da fansho a Najeriya.
Ya ce aiwatar da albashin mafi ƙanƙanta na Naira 70,000 cikin gaggawa, da biyan albashi da fansho a kan lokaci, tare da biyan haƙƙoƙin masu ritaya ba tare da jinkiri ba, sun jawo hankalin gwamnatocin jihohi da dama da ke aikowa da tawaga domin nazari da koyo daga tsarin Jigawa.
Babban Akantan ya tabbatar da ƙudurin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ci gaba da inganta walwalar ma’aikata masu aiki da masu ritaya, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa Hukumar Fansho domin ta cika aikinta yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa, Dakta Binyaminu Shittu Aminu, ya bayyana cewa kimanin Naira biliyan 1.5 ne za a raba ga mutane 564, waɗanda suka haɗa da masu ritaya, iyalan ma’aikatan da suka rasu suna kan aiki, da kuma iyalan ’yan fansho da suka rasu suna karɓar fansho.
Dakta Binyaminu ya ce kimanin Naira biliyan 1.2 daga cikin kuɗin za a biya ga tsofaffin ma’aikata 485 da suka yi ritaya, yayin da sauran kuɗin za a biya wa iyalan waɗanda suka rasu a bakin aiki da kuma iyalan ’yan fansho a matsayin ragowar kuɗaɗen fanshon mutuwa.
Ya kuma sake jaddada ƙudurin hukumar na biyan fansho kowane wata tun daga ranar farko ta kowane wata.



